Home Labarai Saurayi ya turo budurwarsa daga bene hawa biyar

Saurayi ya turo budurwarsa daga bene hawa biyar

51
0

Rundunar ‘yansanda a jihar Anambra ta ce ta cafke wani matashi mai suna Nonso Eze dan shekara 37 da ake zarginsa da turo budurwarsa daga wani bene mai hawa biyar.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar kusa da Orakwe Close 6, Awada Obosi, a karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar, kamar yadda PREMIUM TIMES ta samu labari.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Haruna ya ce “Mista Eze ya tunkudo yarinyar, wadda har yanzu ba a gano asalin ta ba, daga ginin da misalin karfe 3 na dare”.

“kazalika ‘Yansanda sun ziyarci inda lamarin ya faru, sun kuma garzaya da yarinyar zuwa asibiti inda aka tabbatar da cewa ta mutu” inji Haruna.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply