Home Labarai Sauye-sauyen da mata ke samu idan suna haila

Sauye-sauyen da mata ke samu idan suna haila

16
0

A yayin da mata suke jinin haila na al’ada da yawansu kan ga wasu sauye-sauye ko su shiga wani yanayi da ba sa gane kansu sosai.

Sai dai ba kowace mace ce ke fusnkantar irin hakan ba, kuma sauyin da ake gani ɗin ma sun bambanta.

Gama-garin alamun jinin haila
Akwai alamun da suka fi zama gama-gari da mafi yawan mata kan shaide su gabanin ko yayin da suke jinin al’ada.

Irin waɗannan alamu sun haɗa da:

Kumburin mama da kuma ɗan zafi-zai da za su dinga yi
fargaba
kumburin ciki
fitowar ƙuraje a fuska da aka fi sani da pimples
ciwon ƙafa da baya da kartar ciki.

Wasu matan kan rikice wajen bambance alamun zuwan al’ada da na ƙaramin ciki, saboda akwai kamanceceniya sosai.

Hakan ya haɗa da kuburin mama da tashin zuciya da yawan fitsari da yawan jin gajiya da rashin zuwan jinin hailar.

Jinin Haila: Abubuwan da suka kamata ki sani kan al’ada da ɗaukar ciki
Lafiyar mata: Yadda tsarki da sabulu ya jawo wa wata mace matsala.

Wasu alamun da ba kowa ke gani ba
Wasu matan kan ji wasu alamun daban kafin ko a lokacin da suke hailar kamar haka:

Sauye-sauye a ɗabi’u
Rashin samun bacci
jiri
kumburin ciki
janyewa daga shiga al’amura
matsalar mayar da hankali kan abu
taurin mama
gajiya.
Waɗannan alamun kan yi tsanani ga wasu matan yayin da wasu kuma suke jin su saisa-saisa.

Sannan wasu kan ji wasu alamun kamar ciwon kai da kumburin ciki da gudawa.

Duk wadannan na faruwa ne sakamakon sauyin da ake samu a sinadaran halitta.

Wasu manyan sauye-sauye
A hannu guda kuma akwai matan da kan yi fama da wasu gagaruman sauye-sauye da a Turance premenstrual dysphoric disorder(PMDD).

A wani shiri da BBC ta taɓa yi kan yanayin da mata ke shiga a lokacin haila an bayyana PMDD da wani yanayi ne mai tsanani da wasu matan kan shiga idan suna haila.

Yanayin na iya sa mata su shiga cikin tsananin damuwa da bakin ciki har ma da tunanin kashe kansu a yayin da suke haila.

An yi kiyasin cewa mace daya duk cikin 20 na shiga wannan yanayin.

A bara ne hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta dauki cutar da muhimanci.

Daga cikin matakan magance cutar har da cire ƙwayayen haihuwa.

Yanayin kan sa mace ta yi fama da wasu abubuwa kamar:

Tsananin damuwa
sauyin a ɗabi’unta
fushi
fargaba
ruɗewa
matsalar rashin mayar da hankali kan abubuwa
rashin nutsuwa
fargaba.
Abin da ya kamata ga duk macen da take fama da waɗannan matsaloli shi ne ta je asibiti don ganin likita, a bata magunguna ko a ba ta shawarwari.

-BBC Hausa

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply