Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yaba da matakin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na sayar da wasu kadarorin gwamnatin kasar ciki har da matatun mai kamar yadda wasu kafafen yada labarun kasar suka rawaito a makon jiya.
Tun dai kafin zaben shekarar 2019 Alhaji Atiku Abubakar ya shelanta cewa muddin ya samu nasarar lashe zaben kasar to zai cefanar da ilahirin matatun man kasar, lamarin da yasa ‘yan kasar da dama suka rika sukar kudirin nasa a wancen lokaci.
โBurina shi ne zaman lafiya da ci gaban Nijeriya, zan yi matukar farin ciki na bayar da shawarwari ga wannan gwamnatin domin ci gaban ฦasarmu da jamaโarta,โ in ji Atiku, kamar yadda wata majiya ta bayyana wa BBC Hausa.
