Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Sayen tikitin jirgin ƙasa na Abuja-Kaduna ya koma ta intanet

Sayen tikitin jirgin ƙasa na Abuja-Kaduna ya koma ta intanet

50
0

Hukumar kula da sufurin jiragen kasan Nijeriya ta samar da kafar sayen tikitin jirgin daga Abuja zuwa Kaduna ta intanet.

An kaddamar da tsarin ne ranar Laraba, ba tare da an gudanar da wani bikin kaddamarwa ba.

A kan wannan ci gaba da aka samu dai, matafiya za su iya sayen tikitin ta intanet tare da gurzo abunsu.

Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa matafiyan za su iya sayen tikitin a tashoshin jirgin kasan ta hanyar amfani da na’urar biyan kudi ta PoS.

Manajan ayyuka na tashoshin layin dogon Abuja zuwa Kaduna Victor Adamu, ya tabbatar da hakan, yana mai cewa wannan tsarin ya soke biyan tsabar kudi a tashoshin jiragen inda za a rika karbar katin cire kudi na ATM ne kadai ba wai tsabar kudi ba daga yanzu.

Ana sa ran wannan tsari zai kawo karshen karancin tikitin da ake fuskanta a tashoshin jiragen kasan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply