Home Sabon Labari Scholes na tantama kan Ighalo

Scholes na tantama kan Ighalo

105
0

Tsohon dan wasan Manchester United Paul Scholes, ya ce yana tantamar ko dan wasann gaba Odion Ighalo zai yi wani katabus a kungiyar.

Ighalo ya koma Uneted ne a zaman aro na watanni shida daga kungiyar Shanghai Shenhua ta China a cikin watan Janairu inda ya ci kwallaye 4 a wasanni 8 da ya buga.

Kwazon da ya nuna ne ya kara masa wasu adadin watanni shida na zama a kungiyar ta firimiya.

Da yake magana da Man U TV, Scholes ya yabawa tsohon dan wasan na Nijeriya kan yadda ya yi saurin sabawa da kungiyar.

United dai zai su dawo buga firimiya ne a ranar 19 ga watan Yuni inda za su tattaki zuwa arewacin London don karawa da Tottenham.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply