Home Addini SCSN ta buƙaci Ganduje ya bada umarnin kashe wanda ya yi ɓatanci...

SCSN ta buƙaci Ganduje ya bada umarnin kashe wanda ya yi ɓatanci ga Annabi

232
0

Majalisar ƙoli ta shari’ar musulunci a Nijeriya, ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano ta aiwatar da hukuncin kisa da aka yanke wa mawaƙin da aka kama da laifin aibanta Annabi Muhammad SWA.

Wata sanarwa da babban sakataren majalisar ƙolin Nafi’u Baba-Ahmad ya fitar a Kaduna ranar Talata, ya ce aiwatar hukuncin zai zama darasi ga sauran jama’a.

Majalisar ƙolin ta kuma gargaɗi masu neman a yi wa mai laifin afuwa tare sa yin kira ga gwamnatin Kanon da kar ta bi ta kansu.

A ranar 10 ga watan Agusta ne dai wata babbar kotun shari’ar musulunci da ke Kano ta yanke wa wani mawaƙi hukuncin kisa saboda kama shi da laifin yin ɓatanci ga Annabi Muhammad SWA.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply