Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi SERAP ta ba Buhari wa’adin kwana 14 ya binciki batan N300bn

SERAP ta ba Buhari wa’adin kwana 14 ya binciki batan N300bn

97
0

Kungiyar yaki da cin hanci ta SERAP, ta yi kira ga shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya gaggauta gudanar da bincike kan sama da Naira biliyan 300 da rahoton bincike na babban mai binciken kudi na tarayya, na shekarar 2017 ya ce an barnatar.

A kan haka, SERAP ta ba shugaba Buhari wa’adin kwana 14, ya umarci babban lauyan tarayya, kuma ministan shari’a, Abubakar Malami da sauran hukumomin yaki da cin hanci, su gudanar da bincike a kan hukumomi da ma’aikatun da rahoton ya ayyana.

A cikin wata takarda da mataimakin Darktan kungiyar Kolawole Oluwadare ya fitar, SERAP ta ce a rahoton binciken na shekarar 2017, akwai zarge-zarge karara, da ke nuna yadda aka barnatar da kudaden al’umma, da kuma yadda aka kashe wasu kudade ba bias ka’ida ba a ma’aikatu da hukumomin.

Oluwadare, ya ce yin binceken tare da gurfanar da wadanda ake zargin zai kara tabbatar da shirin gwamnati, na yaki da cin hanci tare da kawo karshen masu aikata laifin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply