DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeWasanniSergio Busquets ya fara aikin horarwa a Barcelona

Sergio Busquets ya fara aikin horarwa a Barcelona

Tsohon dan wasan tsakiya na Barcelona da tawagar Spain, Sergio Busquets, ya buɗe sabon babi a rayuwarsa ta kwallon kafa, bayan komawarsa Barcelona a matsayin mataimakin mai horas da ƙaramar kungiyar Barcelona B, wato Barça Atlètic.

Rahoton da gidan talabijin na TVC News ya wallafa ya ce Busquets zai kasance cikin tawagar masu horas da matasan Barcelona, inda zai yi aiki tare da kocin kungiyar, Juliano Belletti.

A cewar rahoton, Busquets zai yi aiki tare da Belletti yayin da yake ci gaba da gudanar da tsarin samun lasisin horar da ‘yan wasa a tawagar.

Busquets mai shekaru 38 ya yi ritaya daga buga kwallon kafa bayan kakar 2025, inda ya shafe kimanin shekaru biyu da rabi yana taka leda a kungiyar Inter Miami ta Amurka.

Kafin komawarsa Amurka, Busquets ya shafe shekaru 15 yana buga wa Barcelona wasa, inda ya zama daya daga cikin fitattun ‘yan wasan tsakiya a tarihin kungiyar.

Ya taso ne daga makarantar koyon kwallon kafa ta Barcelona, sannan ya fara taka leda a Barcelona B kafin daga bisani ya samu damar shiga babbar kungiyar a shekarar 2008.

A tsawon rayuwarsa a Barcelona, Busquets ya lashe manyan kofuna da dama, tare da taka muhimmiyar rawa a nasarorin kungiyar a gasar La Liga da Champions League.

Ya kuma shahara wajen hada kai a tsakiyar fili da Xavi Hernandez da Andres Iniesta.

Masana na hasashen yanzu aikinsa a Barça Atlètic zai ba shi damar fara koyon dabarun horar da ‘yan wasa a aikace, musamman wajen aiki da matasan da ke shirin ɗagawa zuwa babbar tawagar kungiyar Barcelona.

Juliano Belletti, wanda shi ma tsohon dan wasan Barcelona ne, ya jagoranci Barça Atlètic tun shekarar 2025. Ya kuma taba horar da kungiyar Barcelona ta ‘yan kasa da shekara 19.

Komawar Busquets Barcelona a wannan karon, ba domin ya sake buga kwallo ba ce, illa dai fara gina sabuwar sana’a a fagen horarwa, bayan shekaru masu yawa da ya shafe yana daga cikin manyan ‘yan wasan kungiyar a baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata