Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya kori kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar Prof Rafael Afonja.
Kazalika, gwmanan ya sauya ma’aikatu ga wasy kwamishinoninsa biyu.
A cikin wata takarda daga sakatariyar gwamnatin jihar, Mrs Olubamiwo Adeosun, ta ce korar kwamishinan ayyukan ta fara aiki ne nan take, inda aka umurce shi da ya hannanta komai ga babban sakatare na ma’aikatar.
