Home Labarai Shariar Zakzaky: Kotu  ta bayar da belin jagoran yan shi’a

Shariar Zakzaky: Kotu  ta bayar da belin jagoran yan shi’a

76
0

A cikin hukuncin da babbar kotun jihar Kaduna ta yanke a safiyar ranar litinin din nan ta amince jagoran ‘yan shi’a Shek Ibrahim Zakzaky da shi da matarsa Malama Zeenatu su tafi kasar Indiya neman lafiya kamar yadda suka bukata tun da farko.

Sai dai kotun ta ce kada a bar shi ya tafi shi kadai.Ta ce akwai bukatar jamian gwamnatin jihar Kaduna su yi masa rakiya.

Mai magana da yawun yan sh’a IMN Ibrahim Musa ya tabbatarwa da wakilin jaridarmu ta DCL Hausa wannan hukunci. Ya ce cikakken bayanin kungiyar ta yan shi’a IMN zai zo nan gaba kadan a cikin takardar da za su fitar.

 

Lauyan gwamnati Dari Bayero ya shaidawa manema labarai cewa sun nuna damuwarsu akan bayar da wannan beli amma kotu ta ce za ta bayar da belin domin idan har wanda ake kara ya mutu to babu wata sharia da za’a iya yi. A don haka ta bayar da belin nasa.

 

A yanzu ke nan Malam Zakzaky zai iya fita zuwa kasar India dazarar ya kammala samun takardun tafiya asibiti.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply