Sharri akai min bana lalata dalibai -Inji Malamin jami’ar Ado Ekiti
Daga ZUD
Dr. Olaleye Aduwo wanda a watan da ya gabata akai ta yada faifon bidiyon sa inda yake tsirara a kokarin da aka ce yake yi na yin jimai da dalibarsa don ya bata maki, ya musanta zargin.
Lakcaran yace wannan yarinya da ta yi masa zargin kawar diyar cikinsa ce a don haka wannan zargin ba gaskiya ba ne. Kawai dai acewarsa, yunkuri ne na bata masa suna ganin cewa yana da kima a cikin jami’ar jihar Ekiti.
Yaya kuke ganin wannan lamari?
