Home Labarai Shehu Sani ya musanta yi wa budurwa kyautar dubu 800

Shehu Sani ya musanta yi wa budurwa kyautar dubu 800

133
0

Sanata Shehu Sani ya musanta cewa ya tura wa budurwa kyautar kudi Naira dubu 800 maimakon Naira dubu 80 da ta bukata.

A shafinta na twitter, wata mai lakabin “Princess Zarah” ta bukaci da a samu wani ya tallafa mata da kudi Naira dubu 80 (80k) cikin gaggawa.

Bayan wannan roko nata, sai Sanata Shehu Sani cikin barkwanci ya rubutu mata …..kkkkk…. har guda tamanin.

Daga bisani ne sai ta saka hoton alamar kudi sun shiga a banki cewa Shehu Sani ya tura mata zunzurutun kudi har Naira dubu 800 a maimakon dubu 80 (80k) da ta bukata.

To sai dai, Sanatan ya fito karara ya musanta wannan batu, inda har ya yi rantsuwa da Allah cewa bai tura wadannan kudade ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply