Home Labarai Shehu Sani ya roƙawa sarki Sunusi yafiya a wajen Ganduje

Shehu Sani ya roƙawa sarki Sunusi yafiya a wajen Ganduje

119
0

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani, ya roƙi gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya yi yafiya ga mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

A wani bayanin da ya wallafa a shafin sa na Twitter, ranar Juma’ar nan, ya roƙi Ganduje ya yafe, ya manta, ya kuma ƙyale sarkin.

Tsohon Sanatan ya kuma tunatar da Gwamnan cewa mulki kayan aro ne wata rana sarkin zai iya yi masa rana.

Sarkin dai na fuskantar wani sabon bincike kan badaƙalar ₦2.2bn na filaye.

A jiya dai ya kamata sarkin ya bayyana a gaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar Kano amma ya nemi a sake ba shi lokaci.

Saidai a ranar Juma’ar nan, hukumar ta ce dole ne sarkin ya bayyana a gaban hukumar don amsa tambayoyi kafin nan da ranar 9 ga watan Maris.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply