Home Labarai Shehu Sani ya umarceni inba alkalai miliyan 4 – Shaida

Shehu Sani ya umarceni inba alkalai miliyan 4 – Shaida

196
0

Wani mai bada shaida Alhaji Sani Dauda, ya shaidawa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa Sanata Shehu Sani ya umarce shi ya bada Naira miliyan guda-guda ga alkalai hudu don su taimakawa shari’arsa.

Tsohon sanatan dai na fuskantar shari’a kan zarge-zarge biyu da ke da alaka da bada cin hanci da damfara, wadda hukumar yaki da cin hanci EFCC ke tuhumar sa.

Mai bada shaidar, wanda lauya mai gabatar da kara Abba Mohammed ya kawo, ya shaidawa kotun cewa sai da ‘yan sanda suka kama shi, shi da iyalansa, kafin su sake shi a ranar 15 ga watan Disambar bara.

Tun da farko wani shaida Bala Ismail, wanda ma’aikacin Dauda ne, ya ce tshoton Sanatan ya zo wajen uban gidansa sau biyar kafin dokar kulle.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply