Home Sabon Labari Shekarar 2020: Majalisar Dokokin Nijeriya ta bukaci a kawo mata kasafin kudi...

Shekarar 2020: Majalisar Dokokin Nijeriya ta bukaci a kawo mata kasafin kudi akan-kari

68
0

Abdullahi Garba Jani

Majalisar dokoki ta kasa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar ta mika ma ta daftarin kasafin kudin shekarar 2020 kafin ‘yan majalisar su dawo daga hutun da suke yi don gabatar musu nan da karshen watan Satumba, lokacin da za su dawo bakin aiki.

Shugabannin Majalisar Dokokin Sanata Ahmad Lawan da Mr Femi Gbajabiamila sun bugi kirjin cewa a zamanin mulkinsu na majalisa, Nijeriya za ta koma tsarin kai daftarin kasafin kudi cikin lokaci, don ‘yan kasar su samu sa’ida.

Ahmad Lawan Shugaban Majalisar Dattijai

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawan Nijeriya Sen. Adedayo Adeyeye, ya fada wa jarida Punch cewa majalisar ta shirya yin aiki kan kasafin kudin 2020 da zarar ta dawo hutun da take ciki.

Sanata Adeyeye ya ce majalisar na bukatar bangaren zartaswa ya yi aiki tukuru don gabatar da kasafin kudin cikin lokacin da aka kayyade.

Mr Femi Shugaban Majalisar Wakilai
Mr. Femi Shugaban Majalisar Wakilan

A watan da ya ganata yayin tantance wadanda fadar shugaban kasa ta aike wa Majalisar don nadawa ministoci, shugaban Majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya bukaci wadanda za a nada ministocin da su ba fadar shugaban kasa hadin kai don ganin an aike wa majalisar da kasafin kudi ba tare da bata lokaci ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply