Home Labarai Shekarau ya caccaki Buhari kan kin sauya hafsoshin tsaro

Shekarau ya caccaki Buhari kan kin sauya hafsoshin tsaro

471
0

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na karya dokar Nijeriya saboda kin sallamar hafsoshin tsaron kasar da wa’adinsu ya riga ya kare.

Shekarau ya bayyana hakan ne ya yin wata hira da gidan talabijin na Channel cikin wani shirin turanci mai taken ‘Sunrise Daily.

Shekarau ya bayyana cewa sanin kowane a cikin kundin tsarin mulki, an bayyana cewa duk ma’aikacin gwamnati da ya shekara 60 da haihuwa ko kuma ya kai shekaru 35 yana cikin aikin to ya ajiye aikinsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply