DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeLabaraiShettima ya dawo Nijeriya bayan halartar taron AU a Angola

Shettima ya dawo Nijeriya bayan halartar taron AU a Angola

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Sanata Kashim Shettima, ya dawo Nijeriya bayan kammala halartar taron musamman na 21 na majalisar shugabannin ƙasashe da gwamnatocin tarayyar Afirka (AU), wanda aka gudanar a Luanda, babban birnin Angola.

Shettima ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban taron, inda Nijeriya ta yi kira da a ƙarfafa hanyoyin da Afirka ke amfani da su wajen dakile rikice-rikice da warware su, tare da ɗaukar matakan gaggawa kan hare-haren kyamar baki da ake ci gaba da kai wa ’yan Afirka da sauran ’yan ƙasashe a Afirka ta Kudu.

A yayin taron, Nijeriya ta kuma yi kira da a samar da hanyoyin samun kuɗaɗe masu ɗorewa domin ƙarfafa tsarin zaman lafiya da tsaro na Afirka.

Gwamnatin Nijeriya ta kuma jaddada buƙatar ƙasashen AU su ƙara ɗaukar nauyin warware matsalolin rikice-rikicen da ke faruwa a nahiyar, tare da bai wa Afirka damar mallakar hanyoyin magance matsalolinta.

Bayan kammala ayyukansa a Angola, Mataimakin Shugaban ya dawo Abuja.

Komawar Shettima na zuwa ne yayin da rashin kasancewarsa a ƙasar ya jawo ce-ce-ku-ce, musamman saboda Shugaba Tinubu shi ma yana wajen ƙasar domin hutu na tsawon makonni uku.

Shugaban jam’iyyar PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya soki wannan yanayi yayin taron G100 da aka gudanar a Abuja ranar Litinin.

Ya yi tambaya kan wanda ke jagorantar ƙasar a lokacin da shugaban ƙasa da mataimakinsa duk ba sa cikin Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata