Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ya ce Nijeriya na buƙatar kamfanonin tsaro domin magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Ya faɗi haka ne a Calabar, lokacin wani taron ganawa da hukumar tsaro ta Civil Defence ta shirya haɗin guiwa da ƙungiyar kamfanonin tsaro masu lasisi a Nijeriya.
Ministan wanda mai taimaka masa a ɓangaren tsare-tsare Ademola Adeyinka ya wakilta, ya yi kira ga kamfanonin tsaron su ɗaura ɗamarar cike giɓin da ake da shi a ɓangaren tsaron ƙasar.
