Home Labarai Shin ko kannywood ta za ta iya samun dan wasan barkwanci Kamar...

Shin ko kannywood ta za ta iya samun dan wasan barkwanci Kamar Ibro?

88
2

Abdullahi Garba Jani

A ranar 9 ga watan Disambar 2014 ne Allah ya yi wa Rabilu Musa Ibro rasuwa, shekaru biyar ke nan.

Ibro, jarumi ne a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood da ya kware wajen barkwanci da nishadantar da masu kallo.

Jaridar Daily Trust ta rubuta wani rahoto na musamman bayan rasuwarsa inda ta ba da rahoton cewa har yanzu ana ta tsugune-tsugunen wanda ake ganin zai iya bin sahun Ibro a harkar Barkwanci.

Sulaiman Bosho, na daya daga cikin wadanda suka taka rawa tare da marigayi Ibro kafin rasuwarsa, wanda har ma sun yi fina-finai irinsu, Dan Ba’ura da Bori.

Rabi’u Daushe ma, na daya daga cikin wadanda ake ganin kamar za su iya gadar marigayi Ibro wajen shirye-shiryen Barkwanci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

2 COMMENTS

  1. Ina Jin dadin kasan cewa tare da wannan shafi domin Muna samun sahihan labaru da,
    Allah ya Kara daukaka wannan jarida DCL HAUSA

Leave a Reply