Shugaban ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin karɓo maganin Covid-19 daga ƙasar Madagascar.
Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban ƙasar na yaƙi da cutar Boss Mustapha ya bayyana haka a lokacin jawabin kwamitin karo na 29 a Abuja.
A makonni uku da suka gabata ne dai shugaban ƙasar Madagascar Andry Rajoelina ya ƙaddamar da maganin wadda cibiyar bincike ta Malagasy ta samar kuma aka yi masa laƙabin COVID Organic.
