Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sake sabunta rajistarsa ta jam’iyyar APC a mazabarsa ta Sarkin Yara da ke garin Daura a Jihar Katsina.
Tawagar wasu kusoshin jam’iyyar ne suka yi rakiyar shugaban kasar a ranar Asabar ciki har da wasu gwamnonin jam’iyyar da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan.
Majiyar DCL Hausa ta ruwaito cewa a ranar Juma’a ne shugaban kasar isa garin Daura domin hawa sahun sabunta rajista a jam’iyyarsa ta APC.
Ana sa ran komawar Shugaban kasar Abuja a ranar Talata.
