Home Sabon Labari Shugaba Buhari zai halarci taro a ƙasar Ingila.

Shugaba Buhari zai halarci taro a ƙasar Ingila.

159
0

Ahmadu Rabe

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja a ranar Juma’a zuwa birnin London domin halartar kaddamar da taron saka hannun jari tsakanin kasashen Afirka da Ingila wanda za a gudanar a ranar Litinin din nan 20 ga watan Janairun 2020.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasar Mr Femi Adesina a Abuja.

Sanarwar ta ce Pirai Ministan Ingila Mr Boris Johnson ne zai karbi bakuncin taron, da ake kyautata zaton hada shugabannin nahiyar Afrika da ‘yan kasuwa don zakulo hanyoyin zuba jari da za su samar da ayyukan yi ga nahiyar da Ingila.

A lokacin ziyarar, shugaba Buhari zai gana da shugaban kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na “Commonwealth Prince Charles a birnin Scotland.

Ana sa ran shugaban kasar zai dawo Nijeriya a ranar Alhamis ta makon gobe.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply