Home Labarai Shugaba Buhari zai kwashe kwanaki 14 a kasar Ingila

Shugaba Buhari zai kwashe kwanaki 14 a kasar Ingila

74
0

Abdullahi Garba Jani

Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya bar kasar Saudiyya inda ya nufi Ingila bayan kammala aikin Umrah.

Kamfani Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ba da rahoton cewa shugaba Buhari ya bar filin jirgin sama na Sarki Abdul’aziz da misalin karfe 1:30 na rana, a ya yin da ya sauka a filin jirgin sama na birnin London da karfe 3:05 na yammacin Asabar.

Rahotanni sun ce kafin gudanar da aikin Umrah, shugaba Buhari ya halarci taron zuba jari na kwanaki 3 a birnin Riyadh daga ranar 29 zuwa 31 ga watan Oktoba, 2019.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply