Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Shugaba Buhari zai mika wa majalisa kasafin kudin badi a makon gobe

Shugaba Buhari zai mika wa majalisa kasafin kudin badi a makon gobe

92
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mika wa majalisar kasa kasafin kudin shekarar 2021 a mako mai kamawa.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ne ya sanar da haka lokacin da ya ke jawabin maraba da dawowa daga hutun da majalisar dokokin ta yi na makonni 8.

Sanata Lawan ya ce shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin ne domin ya yi saurin samun amincewar majalisar ta yadda zai zama doka.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply