Home Labarai Shugaba Buhari zai tafi kasar Mali

Shugaba Buhari zai tafi kasar Mali

90
0

Shugaban Najeriya Miuhammadu Buhari zai tafi Bamako babban birnin ƙasar Mali a ranar Alhamis.

Tafiyar ta shugaban ƙasar ta biyo bayan tattaunawarsa da Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda yana daga cikin masu shiga tsakani daga ƙunigyar ECOWAS da suka je Mali domin kawo sasanci.

Wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Yammacin Afrika irin su Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou sun amince su hadu a Mali domin tattaunawa domin kawo sasanci tsakanin Shugaban Mali Boubacar Keita da kuma ‘yan adawa a ƙasar.

Ana sa ran Shugaban Ghana Nana Akufo Addo da kuma na Cote d’Ivoire Alassane Ouattara za su halarci tattaunawar.

Bbc Hausa

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply