Home Kasashen Ketare Shugaba Isuhu na Nijar ya ziyarci matan da sojojinsu ke fagen daga

Shugaba Isuhu na Nijar ya ziyarci matan da sojojinsu ke fagen daga

83
0

Yakuba Umaru Maigizawa

A jiya asabar ne shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Alhaji Isufu Mahamadu ya kai wata ziyarar aiki a yankin Diffa mai fama da matsalar tsaro.

Shugaban dai bayan saukar shi a filin jirgin sama na birnin Diffar ya samu tarba daga al’ummar jihar, kama daga hukumomin bariki da shugabannin da ma sauran al’ummar gari.

Da saukar shi dai, shugaban ya fara da ziyartar barikin sojoji inda ya yi jawabin karfafa guiwa a gaban jami’an tsaron da kuma yaba musu irin kokarin da suke wajen yakar ‘yan ta’addar Boko Haram da jihar ke fuskantar hare-hare daga gare su.

Shugaba Isufu Mahamadu ya ziyarci matan sojojin kafin daga bisani ya zarce zuwa Gueskerou kauyen da ke da nisa km 35 da garin na Diffa dan jajanta wa al’ummar yankin da suka fuskanci matsalar ambaliyar ruwan tabkin Komadougou Yobe a kwanakin baya, matsalar kuma da ta tilasta ma al’umma kaurace ma garin.

Sai dai a kan hanyar shi ta tafiyar, shugaban ya yada zango a dukkan garuruwan da ke kan hanya dan gaisawa da al’ummar garuruwan da suka fito bakin titi domin tarbar shi.

Bayan dawowar shi garin na Diffa kafin ya fice sai da ya jagoranci wani taron gaggawa na majalisar tsaro tare da manya-manyan sojojin.

Wannan ziyara dai ita ce irinta ta farko da shugaban ya kai tun bayan zarcewarsa a kan karagar mulki a shekarar 2016 ta biyo bayan kiraye-kiraye da korafe-korafe da al’ummar yankin suka sha yi na rashin ziyarar shugaban a yankin nasu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply