Home Coronavirus Shugaban ƙasa ya ɗora wa kansa alhakin yaɗa Covid-19

Shugaban ƙasa ya ɗora wa kansa alhakin yaɗa Covid-19

82
0

Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera ya ce yana daga cikin masu alhakin bazuwar cutar Covid-19 da ke ci gaba da yaduwa baya bayan nan a kasar.

A wani jawabi da ya yi wa ‘yan kasar ta Radiyo, Chakwera ya ce akwai rashin bin ka’idojin kariya daga yaduwar cutar a tsakanin jam’ar kasar ciki kuwa har da shi kansa.

A makon da ya gabata ne dai Shugaban kasar ya fuskanci kakkausar suka lokacin da wasu hotuna da ke nuna yadda ya ziyarci wani mawaki Madonna suka rika musabaha da daukar hotuna ba tare da bada tazara ko saka takunkumi ba, suka rika yawo a kasar.

A ‘yan makonnin nan masu mutuwa sakamakon cutar a Malawi na karuwa cikin sauri, musamman manyan mutane

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply