Home Kasashen Ketare Shugaban ƙasa ya yi martani kan naɗa ƴan uwa ministoci

Shugaban ƙasa ya yi martani kan naɗa ƴan uwa ministoci

133
0

Sabon shugaban ƙasar Malawi Lazarus Chakwera ya maida martani kan masu sukar tsarinsa na naɗe naɗen majalisar zartaswarsa.

A cikin naɗe naɗen da ya yi dai, akwai ƴan gida ɗaya, miji da mata da kuma manyan ƴan kasuwa a ƙasar.

Lazarus, ya naɗa tsohon abokin takarar sa a zaɓen 2019 Sidik Mia a matsayin Ministan sufuri, sannan ya naɗa matarsa Abida Mia a matsayin mataimakiyar Ministan ƙasa.

Wannan batu dai ya janyo cecekuce a ƙasar, saidai a ganin sabon shugaban ƙasar, yana da dalilinsa na yin hakan.

Shugaban ƙasar ya shaidawa shirin BBC Focus on Africa cewa, ba wai alaƙar waɗanda ya naɗan za a duba ba, saidai nasarorinsu, da kuma abun da za su iya kawowa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply