DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeSiyasaShugaban APC na kasa ya gana da Sarkin Kano Sanusi II a...

Shugaban APC na kasa ya gana da Sarkin Kano Sanusi II a fadar Rumfa

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, a fadar Rumfa da ke Kano ranar Asabar.

Ganawar ta gudana ne a ranar 22 ga Agusta 2026, a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara zafafa a ƙasar nan gabanin babban zaɓen 2027.

Wani na kusa da Sarkin Kano, Muhammad Dallatu, ne ya tabbatar wa jaridar Punch yadda ganawar ta wakana, inda ya ce Yilwatda ya gana da Sarkin ne a wani zaman sirri jim kaɗan bayan dawowar basaraken daga Abuja.

Ziyarar ta zo ne a lokacin da rikicin masarautar Kano ke ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce tsakanin ɓangarorin siyasa da na masarautar jihar.

Rikicin wanda masana suka ce ya samo asali ne daga matakin gwamnatin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, a shekarar 2019, lokacin da aka raba masarautar Kano zuwa masarautu biyar tare da tsige Sanusi daga sarautar Kano.

A lokacin da aka naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin Kano na 15, lamarin da ya haifar da babban rikici tsakanin masu goyon bayan ɓangarorin biyu.

Sai dai a shekarar 2024, gwamnatin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ta soke dokar da ta kafa masarautun biyar, tare da maido da masarautar Kano a ƙarƙashin Sanusi.

Bayan dawo da shi kan karagar mulki, Sanusi ya koma matsayin sarkin Kano na 16. Sai dai matakin bai kawo ƙarshen rikicin ba, domin Aminu Ado Bayero ya ci gaba da samun goyon bayan wasu masu ruwa da tsaki na siyasa da na gargajiya a ciki da wajen jihar.

Masu goyon bayan ɓangaren da ke da alaƙa da gwamnatin Ganduje sun ci gaba da mara wa Bayero baya, yayin da gwamnatin Kano ke ci gaba da goyon bayan Sanusi.

Rikicin ya kuma haifar da ƙalubalen shari’a da na siyasa, inda ɓangarorin biyu ke ci gaba da ikirarin halaccin matsayinsu da kuma na sarkin da suke goyon baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata