Home Kasashen Ketare Shugaban China ya ziyarci Wuhan a karon farko

Shugaban China ya ziyarci Wuhan a karon farko

78
0

Shugaban kasar China Xi Jinping ya ziyar ci Birnin Wuhan inda cutar corana ta samo asali, don nuna cewa kasar na kan shawo kan matsalar.

Ziyarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da China ta samu karancin wadanda suka kamu da cutar zuwa mutum 19 a ranar Talatar nan, kuma dukkan su a Birnin Wuhan ne, in banda mutum biyu da suka zo daga kasashen waje.

Mutum 80,754 ne dai suka kamu da cutar a China yayin da 3,136 suka mutu.

Wannan ziyara dai ita ce ta farko da mista Xi ya kai Wuhan tun bayan barkewar cutar.

Kafafen yada labaran kasar sun ce Mista Xi ya je Birnin ne a ranar Talatar nan, don duba aikin bada kariya da kuma takaita yaduwar cutar, da ke gudana a yankin.

Shugaban kasar ya kuma ziyarci asibitin Huoshenshan, wanda aka gina cikin kwanaki 10 don kula da wadanda suka kamu da cutar, inda ya duba yanayin ma’aikata, kayan aiki da kuma yadda ake gudanar da aiki a asibitin.

Masu sharhi na ganin wannan ziyarar tasa dai a matsayin wata babbar alama da ke nuna kasar na gab da fita mawuyacin halin da ta shiga na barkewar cutar.

Haka kuma, ziyarar tasa ke da wuya kafafen yada labaran kasar suka sanar da rufe asibitoci 14 na wucin gadi da aka kafa silar barkewar cutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply