Home Labarai Shugaban INEC ya sauka daga mukaminsa.

Shugaban INEC ya sauka daga mukaminsa.

338
0

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bar kujerarsa bayan kammala wa’adinsa na farko a ofis Litinin din nan.

Sakamakon haka, an nada kwamishina a hukumar, Ahmed Muazu don ya ci gaba da jagorantar hukumar na riko har zuwa lokacin da majalisar dattawa za ta sake tabbatar da sunan farfesa Yakubu da a karo na biyu.

A karshen watan Oktoban da ya gabata ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya sake aika wa majalisar kasa sunan Farfesa Mahmoud Yakubu don ya ci gaba da shugabantar hukumar idan har ya samu amincewar majalisar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply