Shugaban karamar hukumar Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja, Samuel Danjuma Shekwolo, ya ce mazauna yankin da ba sa goyon bayan jam’iyyar APC su fice daga karamar hukumar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Shekwolo ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ya ce ba zai amince da adawa da jam’iyyar APC ko kuma yunƙurin hana shugaban ƙasa Bola Tinubu sake lashe zaɓe a yankin Kuje ba.
Ya ce mazauna yankin ya kamata su goyi bayan APC saboda ayyukan ci gaba da gwamnatin Tinubu da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, suka aiwatar a karamar hukumar.
Shugaban karamar hukumar ya ce matsayinsa kan batun ba zai sauya ba, yana mai jaddada cewa ba zai amince da mutanen da za su ci moriyar ayyukan gwamnati sannan su juya baya ga APC a lokacin zaɓe ba.
“Na sha faɗa wa mutanen karamar hukumata cewa ko dai kana tare da APC ko kuma ka fice daga wannan karamar hukuma. Ba na jayayya a kan wannan batu,” in ji Shekwolo.
Ya kuma ce, “Ba zan iya ganin minista da shugaban ƙasa suna ayyukan da suke yi, sannan ranar zaɓe ka ce kana son ka yi adawa da mu ba. Ba zan amince da hakan ba. Ko dai kana tare da mu ko kuma kana gaba da mu.”
Kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu suka bayyana su a matsayin barazana ga ‘yancin ‘yan ƙasa da tsarin dimokuraɗiyya, yayin da wasu kuma suka yi kira ga hukumomin tsaro da su sanya ido kan irin waɗannan kalamai yayin da ƙasa ke tunkarar babban zaɓen 2027.
