Home Labarai Shugaban Kasar Guinea ya samu sarautar gargajiya a Daura, jihar Katsina

Shugaban Kasar Guinea ya samu sarautar gargajiya a Daura, jihar Katsina

55
0

Daga Abdullahi Garba Jani/Rahama Ibrahim

 

Sarkin Daura Alh Umar Faruq Umar ya ba shugaban kasar Guinea Alpha Conde sarautar Talban Daura.

Sarkin ya ce, masarautar ta yanke shawarar ba shi wannan sarauta ne, duba da yadda ya ke kaunar shugaban Nijeriya Muhammad Buhari.

Kazalika sarkin ya ce, Alpha Conde ya samu wannan sarauta ne, bisa yadda bai raba daya biyu tsakanin Nijeriya da kasarsa ta Guinea.

Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari a wajen ba da sarautar, ya yaba wa sarkin da ya ba shugaban kasar Guinea wannan sarauta.

Shugaba Buhari da ya samu wakilcin gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya bayyana sarkin a matsayin dattijon da ya san ya kamata, mai fafutikar kawo zaman lafiya ga kasa.

A rahoton da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya fitar ya nuna cewa,wasu daga cikin manyan majalisar masarautar ne suka nadawa Conde rawani ,inda Sarkin Daura ya bashi doki .

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply