Home Kasashen Ketare Shugaban kasar Togo na neman tsayawa takara a wa’adi na 4.

Shugaban kasar Togo na neman tsayawa takara a wa’adi na 4.

90
0

Abdullahi Garba Jani

Kasar Togo za ta gudanar da babban zabenta a watan Fabrairun 2020 a dai dai lokacin da shugaban kasar Faure Gnassingbe ke neman tsayawa takara a wa’adi na 4.

Jaridar Punch ta rawaito cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa ne a ranar 22 ga watan Fabrairu da sharadin komawa zagaye na biyu idan babu dan takarar da ya samu kason kuri’un da ake bukata.

Gnassingbe ya kasance saman karagar mulkin kasar kusan shekaru 15 tun da ya gaji mahaifinsa Eyadema Gnassingbe da ya jagoranci kasar kusan shekaru 38.

‘Yan kasar Togo da ke zaune a kasashen ketare a karon farko, za su kada kuri’arsu a ofisoshin jakadancinsu.

A ranar 6 ga watan Fabrairun dai ne za a fara gangamin neman zabe, a karkare a ranar 20 ga wata.

Jam’iyyun adawa da kumgiyoyin fararwn hula sun yi kira da a dage zaben don ba su damar su sake shiri.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply