Home Labarai Shugaban ma’aikatan Buhari ya gana da kwamitin da ke binciken Magu

Shugaban ma’aikatan Buhari ya gana da kwamitin da ke binciken Magu

130
0

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Nijeriya Farfesa Ibrahim Gambari ya gana da kwamitin shugaban kasar wanda ke binciken zarge-zargen da ake yiwa dakataccen shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya ruwaito cewa, har zuwa lokacin hada wannan labari, ba a bayyana makasudin ganawar Gambari da kwamitin wanda Alkali Ayo Salami ke jagoranta ba.

Tun da farko dai, wata majiya daga fadar shugaban kasar ta tabbatar da an dakatar da Magu a ranar Talata, biyo bayan binciken da kwamitin ke ci gaba da yi masa.

A cewar majiyar, an yi dakatarwar ne dai, domin bada damar bincike kan laifukan da ake zargin sa a kan su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply