Allah Ya yi wa Dr. Babagana Wakil shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Borno rasuwa bayan fama da rashin lafiya.
A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamna Zulum, Mal Isah Gusau, ta ce za a yi jana’izarsa da yammacin Larabar nan.
