Rahotanni daga fadar gwamnatin jihar Kwara sun tabbatar ta rasuwar Aminu Lagun mai kimanin shekaru 73, wanda kafin rasuwarsa shi ne Shugaban ma’aikata a fadar gwamnatin jihar ta kwara.
Mai taimaka wa gwamnan jihar fannin watsa labarai Olayinka Fafoluyi ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook. Sai dai ba a bayyana ko mi nene sanadiyar rasuwar Aminu Lagun din ba.
