Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Abdulaziz Garba Gafasa da shugaban masu rinjaye na majalisar, sun yi murabus daga mukamansu.
Garba Gafasa ya sanar da hakan ne a cikin wata wasika da ya rubuta zuwa ga akawun majalisar, mai dauke da kwanan wata 14 ga Disamba.
Shugaban majalisar yace ya yi murabus ne saboda wasu dalilai na kashin kansa, ya yin da shi kuma shugaban masu rinjaye har yanzu bai yi magana kan dalilan nasa ba.
