Shugaban majalisar dokokin jihar Neja Bawa Wuse da Akawun majalisar dokokin Mohammed Kagara sun kamu da cutar corona.
Kwamishinan watsa labaran jihar Mohammed Idris ne ya tabbatar da labarin ga manema labarai a birnin Minna.
Mohammed Idris bai ba da cikakken bayani dangane lamarin ba, amma dai ya tabbatar da labarin.
