Daga Sharifudeen Ibrahim Muhammad
Hukumar yaƙi da cin hanci da yiwa tattalin arziƙin ƙasa tu’anniti (EFCC), reshen Sokoto ta ce ta kama shugaban Ƙungiyar Manoma Shinkafa ta ƙasa reshen ƙaramar Hukumar Gumi dake Jihar Zamfara, da ke arewa maso yammacin Nijeriya, Rajia Ibrahim kan zargin karkatar da taki da kuma magungunan ƙwari da suka kai darajar naira miliyan 17,100,000.
Shugaban sashin hukumar dake Sokoto, Abdullahi Lawal ya bayyana hakan ga manema Labarai, yana mai cewa wasu ƙungiyoyi bakwai dake ƙarƙashin ƙungiyar manoma Shinkafa ta Gumi ne suka gano badaƙalar.
Yace ƙungiyoyin suna zargin Ibrahim da karkatar da takin zamani tirela uku da maganin ƙwari kanta ɗaya wanda ƙungiyar manoma shinkafa ta ƙasa ta aike masu.
Hukumar ta ce wanda ake zargin ya haɗa kai ne da mai kula da ɗakin ajiya na ƙaramar hukumar Aminu Musa, inda suke sayar da taki ga wani ɗan Kasuwa mai suna Abdullahi Bashir.

Bugu da ƙari, Shugaban na EFCC a yankin ya ce, wannan bincike ya biyo bayan wasiƙar koke da hukumar ta samu daga wasu al’ummomi bakwai da suka hada da Ruwan Giginya, Gawon Gulibi, Gambosi, Yar’panawa, Garka Bala Masinja, Lemawa tare da Sabon Gari duk a cikin Karamar Hukumar Gumi a Jihar Zamfara.
