Home Kasashen Ketare Shugabannin kasashen yankin Sahel na gudanar da taron gaggawa a Nijar

Shugabannin kasashen yankin Sahel na gudanar da taron gaggawa a Nijar

68
0

A dazu dazun nan ne shugabannin kasashen yankin Sahel guda biyar(5) da suka hada da na Burkina Faso da na Mali da na Mauritaniya da na Tchadi da na Nijar mai masaukin baki suka hallara a birnin Yamai dan gudanar da wani taron gaggawa na kungiyar.

A yanzu haka dai shugabannin na can na tattaunawa dan lalubo mafita bisa kan matsalolin tsaro da suka addabi yankin na Sahel.

Wannan kuwa ya biyo bayan wannan mummunan hari da aka kai ma sojojin Nijar da ya yi sanadiyar rasa rayukan sojojin 71. Sai dai gabanin fara taron shugabannin sun halarci makwanta sojojin dan yi musu addu’a.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply