Home Kasashen Ketare Shugabar hukumar zaben kasar Malawi ta yi murabus

Shugabar hukumar zaben kasar Malawi ta yi murabus

147
0

Matar da ta ke Shugabantar hukumar zaɓen ƙasar Malawi ta yi murabus daga muƙaminta wata ɗaya kafin a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu.

wata Kotun kasar ce ta bada umarni da a sake gudanar da zaɓen bayan ta soke na shekarar 2019, wanda ya bai wa Shugaba Peter Mutharika damar mulki karo na biyu.

Tun kafin yin murabus din Jane Ansah an samu masu zanga-zanga da sukai ta kira da ta sauka, suna masu cewa ta gaza a zaɓen farko, ya yin da suka zarge ta da yin magudi, ta hanyar sauya alkaliman zaben wajen yin amfani da inki wajen gyara takardun kaɗa ƙuri’a.
Za a yi zaɓen ranar 23 ga watan Yuni.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply