Jinyar Idris Moda: SHUGABANNIN KUNGIYAR MAAIKATAN GIDAN REDIYO, TALABIJIN DA WASAN KWAIKWAYO SUN KAIWA MODA ZIYARA.
Shugaban RATTAWU na kasa Dr. Kabir Garba Tsanni shi ne ya jagoranci tawagar zuwa wurin fitaccen mai wasan Hausan nan Idris Moda.
Idris Moda yayi fama da rashin lafiyar da a kwanakin baya wasu suka rika yada cewa ya mutum. Amma daga bisani labarin ya zama na kanzon-kurege.
A cikin wannan watan ne kuma aka yankewa dan fim din kafa a sakamakon ciwon da ke damunsa.
