Home Labarai Siyasa: An daidaita tsakanin Yari da Marafa

Siyasa: An daidaita tsakanin Yari da Marafa

27
0

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari da Sanata Kabiru Garba Marafa, dukansu ‘ya’yan jam’iyyar APC sun yi sasanci ya ka junansu sun dinke barakar siyasar da ke tsakani.

DCL Hausa ta gano cewa an cimma wannan sulhu ne bayan wani zaman sasanci da aka gudanar a Kaduna. Dukkaninsu dai sun gana da Gwamna Mai Mala Buni shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC na kasa a makon jiya.

Dukkaninsu dai sun aminta su rusa tsagin jam’iyyar da kowa ya kafa, suka koma karkashin inuwa daya wadda Abdul’aziz Yari ya zamo jagoranta. Bugu da kari sun kafa kwamiti mai mutane 13 da zai cigaba da bibiya domin dinke barakar jam’iyyar a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply