Home Sabon Labari Siyasa: Kotu ta kori karar wasu yan takarar Majalisa 3 a Oyo

Siyasa: Kotu ta kori karar wasu yan takarar Majalisa 3 a Oyo

62
0

Saleem Ashiru Mahuta/Banye

 

Kotun sauraron kararrakin Zaben Yan Majalisar tarayya da na Jihohi da ke zaman ta a Jihar Oyo dake Kudu Maso Yammacin Nieriya, a jiya  Asabar ta kori karar da dan takarar jam’iyyar PDP Ademola Omotosho ya shigar gabanta yana kalubalantar zaben da akayi wa Olaide Akinremi na Jam’iyyar APC a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ibadan ta Arewa a Majalisar Tarayyar kasar.Jaridar Dailytrust ce ta byar da wannan rahoto.

 

Haka kuma kotun ta kori karar da Mugbonjubola Olawale na Jamiyyar PDP a mazabar Oluyole akan abokin karawarsa Tolulope Sadipe na APC, da kuma karar da Farfesa Joseph Adeniyi na jam’iyyar APC ya shigar akan nasarar da Oluyemi Taiwo na PDP ya samu darewa bisa kujerar danmajalisar tarayya mai wakiltar mazabun Ibarapa  ta Gabas da Ido.

 

A cikin mabambantan hukunci da mutane uku suka yanke a kotun, wanda mai-shari’a Anthony Akpovi yake jagoranta tare da mambobi biyu wanda ya hada da mai shari’a Sambo Daka da mai shari’a Chinyere Ani sun kori kararrakin 3 da aka shigar gaban kotun.

 

A ta bakin masu karar, sun ce sun shigar da karar ne duba da yadda aka gudanar da zaben ba bisa ka’ida ba wanda yake cike da kurakurai wanda a cewarsu hakan yasa suke ganin ba’a bi ka’ida wajen bayyana wadanda suka ci zaben ba, a don haka ne suka nemi kotun da ta tabbatar da su a matsayin wadanda suka samu nasarar zaben ko kuma soke zaben gabadaya.

 

Da suke yanke hukunci alkalan sun karanta cewar, kotun ta gano cewar karar ba ta da karfi a don haka ta bukaci a biya Naira 150,000 ga kowanne mai karar. Haka zalika, kotun ta bayyana cewar babu inda ba’a samun kura kurai a duniya a yayin zabe, tana mai bayyana cewa, masu karar sun kasa bayar da kwakkwarar hujja domin tabbatar da abinda suke zargi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply