Home Sabon Labari Siyasar Kano: APC ta dakatar da Abdulmumin Jibrin

Siyasar Kano: APC ta dakatar da Abdulmumin Jibrin

98
0

Daga Abdullahi Garba Jani

Jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano, ta dakatar da dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kiru/Bebeji a jihar Kano a Majalisar wakilai ta kasar.

Jaridar *_Daily_* *_Nigerian_* ta wallafa cewar jam’iyyar ta dakatar da Abdulmumin Jibrin ne bisa zargin zambo-cikin-aminci ga jam’iyyar APC.

A wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Bebeji, Sulaiman Gwarmai da aka raba wa manema labarai a kano, ta ce dakatarwar ta zamo wajibi, ganin yadda shi da kanshi dan majalisar ya tabbatar da aiwatar da wadannan ayyukan da ke nuna kin jinin jam’iyyar.

Takardar dakatar da Dan Majalisar

Shi dai Sulaiman Gwarmai bai fadi irin ayyukan da ake zargin Abdulmumin Jibrin da aikatawa ba, amma ya ce sun ci karo da kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Ya ce an cimma yarjejeniyar dakatar da dan majalisar ne biyo bayan duba shawarwarin da wani kwamiti mai mutane 7 da aka kafa don binciken lamarin ya bada.

Shugaban jam’iyyar ya bukaci reshen jam’iyyar na jihar da ya bi kadin lamarin har matakin kasa, don ganin uwar jam’iyya ta kasa ta kore shi baki daya.

Abdulmumin Jibrin dai na daya daga cikin na gaba-gaba wajen goyon bayan shugaban majalisar wakilai, Mr. Femi Gbajabiamila musamman ma lokacin da za a gudanar da zaben shugabancin Majalisar.

Sanarwar dakatar da dan majalisar ta zo yan kwanaki bayan an fitar da sunayen shugabannin kwamitocin Majalisar Wakilai ba tare da sunansa ba duk aikinyi da ake ganin ya yiwa kakakin Majalisar

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply