Home Kasashen Ketare Sojoji 20 sun mutu a Kasar Afghanistan

Sojoji 20 sun mutu a Kasar Afghanistan

90
0

Rahotanni na cewa, akalla jami’an soji 20 suka rasa rayukan su a wani hari da ‘kungiyar tada ‘kayar-baya ta Taliban ta kai cikin dare a yankin Jawzjani da ke Arewacin Kasar Afghanistan, yayin da wasu jami’an soji 2 suka ‘bace biyo bayan wani hari da a ka kai sansanin soji da ke yankin Aqchah.

Dan Majalisa mai wakiltar yankin Mohammed Karim Jawzjani tare da mamban hukumar gudanarwa suka bayyana hakan inda suka ce Kungiyar Taliban a yanzu haka sun kwashe fiye da watanni hudu suna rike da gundumomin Qustepa tare Darzab.

Yanzu haka dai Jami’an sojin Kasar Afghanistan na cigaba da fafatawa da ‘yan aware tare da ‘Yan Kungiyar IS.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply