Home Labarai Sojoji 356 sun aje aiki – sun ce aikin ya ginshesu

Sojoji 356 sun aje aiki – sun ce aikin ya ginshesu

334
1

A ƙalla sojoji 356 ne daga yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya da sauran sassan ƙasar suka aike da takardar neman ajiye aiki ga babban Hafsan sojin ƙasar Laftanar Janar Tukur Buratai.

Da yawa daga sojojin da suka aike da buƙatar ajiye aikin a ranar 3 ga watan Yulin 2020, sun bada dalilan cewa aikin ya ginshesu.

Buratai, ya kuma amince da ajiye aikin sojojin 356 a wata takarda mai shafi 17 da lamba AHQ DOAA/G1/300/92 wadda Brig. Gen. T. E. Gagariga ya sanyawa hannu.

Wasu majiyoyin tsaro sun nuna cewa dakarun sojin, waɗanda yawancin su daga Arewa maso Gabas suka fito, sun aje aikin ne saboda rashin samun ƙwarin giwa, makamai, ƙarin kuɗin alawus da kuma yadda ƴan Boko Haram ke kashe sojojin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply