DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeLabaraiSojoji na neman hana ni shiga Osun – Davido

Sojoji na neman hana ni shiga Osun – Davido

Fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi zargin cewa wasu sojoji na ƙoƙarin hana shi shiga jihar Osun yayin da ake gudanar da zaɓen gwamnan jihar a yau, Asabar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Davido, wanda ɗan’uwan Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ne, ya bayyana zargin ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Mawakin ya ce an sanar da shi cewa sojoji na ƙoƙarin hana shi shiga jihar, yana mai jaddada cewa kowane ɗan Nijeriya na da ’yancin zirga-zirga a cikin ƙasar.

Sai dai zargin nasa ya zo ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro suka sanya dokar hana zirga-zirga a faɗin jihar Osun saboda zaɓen gwamnan jihar.

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa an takaita zirga-zirga a jihar daga ƙarfe 12:00 na daren Juma’a, 14 ga Agusta, zuwa ƙarfe 6:00 na yammacin Asabar, 15 ga Agusta.

Hukumomin tsaro sun ce matakin na daga cikin shirye-shiryen tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana da tsari, inda aka jibge dubban jami’an tsaro a sassan jihar.

Davido ya kasance cikin waɗanda suka taka rawa wajen yaƙin neman zaɓen kawunsa, Gwamna Ademola Adeleke, wanda ke neman wa’adi na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar Accord.

Zargin nasa ya jawo martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu suka ce mai yiwuwa bai yi la’akari da dokar takaita zirga-zirgar da aka sanar ba.

Tsohon mai taimaka wa shugaban Nijeriya kan harkokin yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana kalaman Davido a matsayin wuce gona da iri, yana mai cewa an riga an sanar da jama’a game da takaita zirga-zirgar.

Ya ce takaita zirga-zirga a lokacin zaɓe ba yana nufin an hana ’yan ƙasa ’yancinsu ba, domin ana sa ran jama’a za su bi matakan tsaro da aka sanya bisa doka domin tabbatar da zaman lafiya da sahihin zaɓe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata