DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 10, 2026
HomeLabaraiSojoji sun cafke ‘yan ta’adda biyu a Zamfara

Sojoji sun cafke ‘yan ta’adda biyu a Zamfara

Sojojin Birged ta 1 ta rundunar sojin Nijeriya da ke aiki daga sansanin soji na Kaura Namoda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da ta’addanci a karamar hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa kamen ya faru ne yayin wani sintiri na dare da sojojin suka gudanar a yankin, bayan sun yi arangama da su yayin sintirin.

Mai magana da yawun Rundunar Sojin, Birged ta 1 da ke Gusau, Yusuf Mohammed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Laraba. Rundunar ta ce mutanen biyu ’yan asalin kauyen Ilela ne da ke karamar hukumar Maradun ta Zamfara.

Sojojin sun kwato bindigar AK-47 guda daya, bindigar Dane da aka kera a gida guda, magazin bindiga biyu da harsasai 55 na 7.62mm. Haka kuma an kwato harsasan Dane 18, babur guda daya, rediyon sadarwa na Baofeng guda biyu da wayar hannu guda daya.

Baya ga haka, rundunar ta ce ta kwato na’urar MP3 guda biyu, rigar kameflaji, hulunan sojoji guda biyu, jaka da kuma N44,500.

Binciken farko da aka yi kan wayar daya daga cikin wadanda ake zargin ya gano hotuna da bidiyoyi da ake ganin za su iya zama muhimmiyar shaida, amma jami’ai na ci gaba da tantance su.

Kwamandan rikon kwarya na Birged ta 1, Kanal J Umaru, ya yaba wa sojojin bisa jajircewa da kwarewa, tare da umartar su da su ci gaba da kai hare-hare da sintiri domin hana ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka damar gudanar da ayyukansu a yankin.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata